na yi nasara, rumgume da kirjina,
na kayar da barci a wannan kokowar,
na yi nasara kan ido mai sanin malam-bude-littafi,
na yi nasarar kayar da gangar jiki
na yi nasarar kame habar kogi,
mai malala ba tare da makamashi ba
—ina maraba da bakona, ta ce;
daren da ba a gamo da raba—dukkan
kofofinta sun san inda na nufa, inda na tafi, ba na
neman gafara, domin kuwa in tsuntsu na yawo,
kere na wulgi, suna da tabbacin
gamuwa da mukaddari
na yi nasara, rumgume da kirjina,
na kayar da barci a wannan kokowar,
na yi nasara kan ido mai sanin malam-bude-littafi,
na yi nasarar kayar da gangar jiki
i win my bosom
i win a sleep that holds
i win an eye that knows butterflies
i win more than a blackbody
i win a coast / that runs
on scarlet fuel ¬
—come to my house, she
replied; there will
be no dews
tonight—all her
doors now know
where i go, where i go, i am
not sorry, the furs
are certain the drawers
will be their time, but
the rest follow
a brook
i win my bosom
i win a sleep that holds
i win an eye that knows butterflies
i win more than a blackbody
Translated from English into Hausa by Ibrahim Malumfashi.